Isa ga babban shafi

Liman Mahmoud Dicko ya cacaki shugaban sojin Mali, Kanar Assimi Goita

Babban Limamin kasar Mali da ya jagoranci zanga zangar adawa da gwamnati bara, Mahmoud Dicko ya cacaki shugaban sojin kasar, Kanar Assimi Goita inda yake cewa al’amura basa tafiya daidai a cikin kasar.

Liman Mahmoud Dicko. na kasar Ghana
Liman Mahmoud Dicko. na kasar Ghana REUTERS/Matthieu Rosier
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a Bamako, Imam Dicko yace yana so ya shaidawa jama’a al’amura basa tafiya daidai, yayin da shugaba Goita yaki ganawa da shi.

Kasuwar babban birnin Bamako
Kasuwar babban birnin Bamako AFP - MICHELE CATTANI
Malamin yace basa tafiya tare shugaban sojin, kuma basa tafiya tare da kasashen duniya, saboda yadda ake nunawa kasar wariya.
Liman  Mahmoud Dicko na kasar Mali
Liman Mahmoud Dicko na kasar Mali © AFP/ Michele CATTANI
Sai dai Imam Dicko yace ba wai kira yake a sake fitowa zanga zanga ba.Kasar Mali na fuskantar takunkumi daga kungiyar ECOWAS da AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya saboda juyin mulkin soji da kuma kin gabatar da shirin mayar da mulki ga fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.