Isa ga babban shafi

Jamus ta dawo da aikin sintirin Sojinta a gabashin Gao na Mali

Rundunar sojin Jamus ta  ce ta dawo da sintiri a gabashin Mali, a cikinn wani aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, bayan dakatarwa da ta yi a lokacin da gwamnatin kasar ta hana ta damar amfani da sararin samaniyarta.

Wasu dakarun Sojin Jamus a Mali.
Wasu dakarun Sojin Jamus a Mali. AFP - JOHANNES EISELE
Talla

A wata sanarwa, wata kakakin sojin Jamus ta ce dakarun kasar sun dawo aikin sintiri a wajen birnin Gao a Talatar nan.

A ranar 12 ga watan Agusta ne ma’aikatar tsaron Jamus ta ce ta dakatar da aikin kiyaye zaman lafiya da take yi a Mali, bayan da gwamnatin kasar ta hana ta daamar amfani da sararin samaniyarta don jigilar sojojin da ke aikin a karkashin rundunar Majalisar Dinkin duniya ta MINUSMA.

A wata sanarwa a Larabar nan, rundunar sojin Jamus ta ce wani bangare na dakarunta da ya isa birnin Gao na a shirye don ci gaba da aiki, kuma   har ya dauki nauyin tabbatar da tsaron sansanin soji na birnin.

Akasarin sojojin Jamus da ke Mali na zaune ne a sansaninsu dake  kusa da wannan biri na Gao.

Rashin jituwa ya samo asali ne bayan da gwamnatin mulkin sojin Mali ta rabu da Faransa ta koma wa Rasha don neman taimako a yakin da take da ta’addanci.

Yakin da ya ki ci ya ki cinyewa ya yi sanadin salwanta dubban rayuka, tare da tilasta wa daruruwan dubbai tserewa daga gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.