Isa ga babban shafi

Ivory Coast ta nemi ECOWAS ta shiga tsakani don tilasta Mali ta saki Sojinta 46

Ivory Coast ta bukaci shiga tsakanin kungiyar ECOWAS don warware takaddamar da ke tsakaninta da Mali game da matakin kin sakin Sojojinta 46 da ke tsare a hannun gwamnatin Sojin Bamako.

Shugaba Alassane Ouattara, na Ivory Coast.
Shugaba Alassane Ouattara, na Ivory Coast. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Wani kwamiti karkashin jagoranci shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara da ke tattaunawa kan kokarin sakin Sojojin 46, ya zargi Mali da kokarin yiwa kasar barazana bayan gindaya mata sharadi kafin sakin Sojin.

Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana cewa akwai bukatar shigowar ECOWAS cikin gaggawa don fara tattaunawa tare da lalubo bakin zaren don sakin sojojin 46.

A makon jiya ne, shugabancin Sojin Mali ya bukaci musayar Sojojin na Ivory Coast 46 da ‘yan siyasar Bamako wadanda Abidjan ke bai wa mafakar siyasa tun bayan juyin mulkin Soji.

Da ya ke gaban taron kwamitin, shugaba Ouattara ya bukaci Mali ta gaggauta sakin Sojojin yayinta nemi kungiyar ECOWAS ta shirya taron kasashe mambobinta cikin gaggawa don tattauna batun.

A cewar Ouattara sam bukatar da Mali ta shigar baa bar karba ba ce, kuma baza su yarda da barazanar da kasar ke musu ba.

Tun ranar 10 ga watan Yulin shekarar nan ne, mahukuntan Mali suka kame Sojojin na Ivory Coast 49 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman Bamako bisa zarginsu da kasancewa sojojin hayar da ke taimakawa wajen kaddamar da hare-haren ta’addanci a sassan kasar.

Sai dai gwamnatin Ivory Coast na ci gaba nanata cewa Sojin na ta sun shiga Mali ne don taimakawa rundunar wanzar da zaman lafiya da ke aiki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.