Isa ga babban shafi

Tawagar Ecowas ta isa Nijar don sasanta rikicin kasar

Tawagarr da Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wato Ecowas ta tura zuwa Nijar ta isa kasar a yunkurin sake da dawo da kasar kan turbar dimokuradiyya. 

Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO
Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Ita dai wannan tawaga da ta sauka a  birnin Yamai, bayanai sun ce tana karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya ne wato Janar Abdul Salami Abubakar da kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, mutanen da ke da cikakkiyar masaniya a game da lamurran da suka shafi Nijar da ma sauran kasashe na yammacin Afirka. 

Tawagar ta isa ne a yayin da manyan kwamandojin soji daga kasashen Afirka ta Yamma suka fara wani taro yau laraba a birnin Abuja, domin fayyace matakan da za su yi amfani da su wajen kaddamar da farmaki domin dawo da Mohamed Bazoum kan mukaminsa da zarar bukatar hakan ta taso. 

To sai dai kamar yadda yake cewa lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin wannan taro da zai kawo karshe ranar juma’a, Kwamishinan Kula da Harkokin Siyasa da Tsaro na Kungiyar Ecowas Abdel-Fatau Musah, za a yi amfani  da karfin soji a kan Nijar ne idan sauran hanyoyi na lalama suka gaza. 

Yau dai mako daya kenan da sojoji karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar kare lafiyar shugaban kasar Janar Abdourahman Tchiani suka sanar da kwace mulki daga hannun shugaba Bazoum, kuma yanzu haka suna ci gaba da yin garkuwa da shugaban da kuma wasu kusoshin gwamnati da na jam’iyyarsa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.