Masu sufuri sun koka bisa yanayin filayen aijye manyan motoci a Nijar
Masu motocin dakon kaya a jamhuriyar Nijar sun bukaci gwamnati ta dawo masu da izinin tafiyar da wuraren ajiye manyan motoci da ake kira Park, wadanda aka danka a hannun ‘yan kasuwa da ba su da alaka da aikin sufuri.
Wallafawa ranar:
Alhaji Hima Barkire, daya daga cikin shugabanni a kungiyar masu motocin sufuri a kasar ta Nijar, ya shaidawa sashin hausa na RFI cewa wuraren ajiye manyan motocin guda biyu ne, kuma ya ce masu zirga zirgar sufuri ne suka hada hannu wajen gininsu.
A cewar Barkire tun a waccan lokacin masu sufurin ke kula da wuraren bayan gina su, sai daga baya ‘yan siyasa suka karbe hakkin kula da wajen suka dankawa wani dan kasuwa da bashi da alaka da harkar ta sufuri.
Barkire ya koka bisa yadda ya ce wuraren ajiye manyan motocin ke cikin rashin kyawun yanayin da yake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu