An gano malaman makaranta na boge sama da 2,000 a Nijar
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa HALCIA ta ce ta gano malaman makaranta na boge 2,565 a cikin jahohi 5 na Jamhurriyar Nijar.
Wallafawa ranar:
Salissou Oubandoma mukadashin jagoran hukumar ya bayyana cewa a duk wata gwamnatin na biyan albashi ga malaman na boge dake cikin jahohin kasar 5 da suka hada Yamai da Dosso da Tahoua sai Agadez da kuma jahar Diffa.
Sauren jahohin 3 da suka hada da Zinder, Maradi, da Tillabery za a bayyana nasu sakamakon binciken na gaba.
An gudanar da binciken ne daga makaranta zuwa makaranta a Jamhuriyar Nijar Kashi 80% na malaman makaranta na aiki ne a karkashin tsarin kwantiragi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu