Masana sun ja hankalin Gwamnatin Nijar kan tattalin arziki
Yayin da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, ke cewa tattalin arzikin kasar yana bunkasa, kuma zai dore cikin wannan hali nan da shekaru biyar masu zuwa, wasu masu nazari na ganin bayanan sun saba da halin da jama’ar kasar ke ciki na matsi.
Wallafawa ranar:
Abdu Dan Neto na wata kungiyar farar hula da ke Maradi, ya ce har yanzu da dama daga cikin jama’a a Nijar suna fama da yunwa, ga kuma rashin kudi a hannun mutane wadanda suka hada da ‘yan kasuwa da ma’aikata.
Yayin da yake tattaunawa da sashin Hausa RFI, Abdu dan Neto ya kamata Gwamnatin Nijar ta sake nazari kan matakin da ta ce ta dauka na tsuke bakin aljihun ta domin saukakawa mutane halin da suke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu