Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan tawayen sudan ta na zargin sojan gwamnati da kai musu hari

‘Yan tawayen kasar Sudan ta Kudu sun soki bangaren Gwamnati da fara karya sharuddan yarjejeniyar sulhu da suka kulla makon jiya, domin maido da zaman lafiya bayan sun kwashe watanni 20 ana gwabza yaki.

'Yan tawayen kasar Sudan ta Kudu
'Yan tawayen kasar Sudan ta Kudu Reuters
Talla

Jagoran ‘yan tawayen Riek Machar, ya shaidawa manema labarai a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cewa sojan Gwamnati sun kaiwa ‘yan tawayen hari a yankin Nile.

A ranar Laraba data gabata ne dai Shugaban Sudan ta kudu Salva Kirr ya amince ya sanya hannu cikin yarjejeniyar zaman lafiya, gudun kasar duniya ta kakaba masu takunkumi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.