Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sojojin Sudan ta kudu sun aikata laifukan Yaki

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin Sudan ta kudu da yi wa Yara kanana fyade da kuma kona mutane da ran su a gidajen su a yakin da su ke fafatawa da ‘Yan Tawayen kasar da ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar
Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar Reuters/George Philipas
Talla

Wani rahoton bincike da aka gabatar wa kwamitin Sulhu ya bayyana cewar irin tashin hankali da ake yi da cin zarafin Bil Adama da kisa da kuma kama halin da fararen hular kasar suka shiga ba a taba ganin irinsa ba, saboda yadda bangarorin biyu ke kokuwar iko.

Shugaban aikin jin kai na majalisar Stephen O’Brien ya shaidawa kwamitin cewar irin muguntar da suka gani karara kan hare haren da aka kai wa fararen hula ya nuna cewar rikicin ya fi karfin na neman madafin iko.

A watan Disemban 2013 ne dai Sudan ta kudu ta fada cikin rikici tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaban kasa Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Rikicin kasar kuma ya rikide ya koma na kabilanci tsakanin kabilar Dinka ta Kiir da kabilar Nuer ta Machar.

A yau Laraba ake sa ran shugaba Salva Kiir zai sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan Machar ya sanya hannu a makon jiya domin kawo karshen rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.