Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya ki sanya hannu kan Yarjejeniyar zaman lafiya

A dazun nan ne ‘yan tawayen Sudan ta Kudu suka sanya hannu kan yarjejeniya zaman lafiya na wucin gadi da ke nuna cewa sun Shirya amincewa da zaman lafiya ta didindin da gwamantin Sudan, yayin da bangaren gwmanati ta bukaci karin kwanaki 15 kafin kulla yarjejeniyar a nan gaba.

shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Yau litinin ita ce ranar karshe da kasashen duniya suka bai wa bangarorin biyu su cim ma jituwa ko kuma a sanya masu takunkumai mai tsananin.

A cewar Jagoran Masu shiga tsakanin bangarorin biyu Seyoum Mesfin Riek Machar ya sanya hannu kan takarda yarjejeniyar, amma Salva Kiir ya bukaci karin lokaci domin sake nazari cikin kwanaki 15 masu zuwa.

Har yanzu dai babu cikakken bayanai kan batutuwan da yarjejeniyar ta kunsa, sai dai Machar ya bukaci hadin kan Kiir domin kawo karshan rikicin kasar.

Kafin wannan zama dai Salva Kiir ya gargadi cewa ba lallai su cimma matsaya nan take ba na didindin, saboda akwai rabuwar kawuna tsakanin ‘yan tawayen kasar.

Akalla sau 7 ana wasti da yarjejeniyar tsaigata wuta a Sudan ta Kudu kwanaki kalilan bayan tsayar da batu guda.

Tun a cikin shekarar ta 2013 rikici ya barke a Kasar a lokacin da Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da kokarin hambarar da shi daga karagar Mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.