Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Amurka za ta dauki mataki akan Sudan ta Kudu

Gwamnatin Amurka tace tana kan tattaunawa da sauran manyan kasashen duniya domin sanya takunkumi ga shugabannin Sudan ta kudu da ke rikici da juna idan har ba su amince da yarjejeniyar samar da zaman lafiya ba.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar
Talla

Tuni dai Amurka da Birtaniya suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa gwamnatin Sudan ta kudu takunkumi kan kin amincewa ta sanya hannu ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ranar litinin domin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar na tsawon shekaru biyu.

Susan Rice mai ba Shugaba Barack Obama shawara kan sha’anin tsaro ta fadi a cikin wata sanarwa cewa za su dauki matakin takunkumi idan har ba a amince da yarjejeniyar ba nan da kwanaki 15.

Shugaban Sudan Salva Kiir ya ki amince da yarjejeniyar a ranar Litinin da shugabannin kasashen Afrika suka tsara.

Sudan ta kudu da ta balle daga Sudan a 2011, ta abka cikin rikici ne a watan Disemban 2013, bayan Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.