Isa ga babban shafi

Saliyo ta fara lalata miyagun kwayoyin da ta kama

Hukumomin Saliyo sun kona muggan kwayoyin da kudinsu ya kai dalar Amurka dubu dari 2, makonni biyu bayan sanya dokar ta baci a bangaren tu’ammuli da muggan kwayoyi da gwamnatin kasar ta yi.

Shugaba Julius Maada Bio, na Saliyo
Shugaba Julius Maada Bio, na Saliyo REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

Bikin kona kwayoyin da ya gudana a Kwalejin horas da ‘yan sanda da ke babban birin kasar Freetown, ya samu halartar da dama daga cikin hukumomin tsaro da kuma al’ummar kasar.

A cewar babban jami’in ‘yan sandan kasar da ke kula da sashin yaki da muggan laifuka Mohamed Alieu, sun lalata magungunan ne saboda illar da suke haifarwa a cikin al’umma.

Shi ma shugaban Hukumar Yaki da tu'ammuli da miyagun kwayoyin ta kasar Andrew Jaia KaiKai, ya ce daga cikin kwayoyin  da suka kona har da hodar ibilis.

Dama dai a farkon watannan ne shugaban kasar Julius Maada Bio, ya ayyana sanya dokar tabaci kan tu’ammuli da miyagun kwayoyi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.