Isa ga babban shafi

RSF ta tsananta hare-hare a kan birnin al-Fashir na arewacin Darfur

Sabbin hare-haren dakarun RSF kan birnin al-Fashir na arewacin Darfur ya sanya fargabar sake fantsamar yakin Sudan na fiye da shekara guda zuwa yankin wanda ke dauke da iyalai akalla miliyan 1 da dubu 600 da suka tserewa matsugunansu.

Ana fargabar hare-haren na birnin al-Fashir ya sake tsananta yakin na Sudan.
Ana fargabar hare-haren na birnin al-Fashir ya sake tsananta yakin na Sudan. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Al-Fashir shi ke matsayin birni mafi girma da baya karkashin ikon RSF a yankin na yammacin Darfur, duk da yadda mayakan na RSF suka mamaye tare da kwace iko da dukkanin sauran sassan Darfur wanda ya kai ga zarginsu da aikya kisan kabilanci kan tsirarun kabilun da ba Larabawa ba musamman a yammacin yankin.

Dubban fararen hula ne da rikicin na fiye da shekara guda ya raba da matsugunansu ke samun mafaka yanzu haka a Arewacin na Darfur, kuma isar rikicin birnin al-Fashir mai tarihi kai tsaye zai sake ta’azzara yakin na Sudan, lura da tasirin yankin wajen ta’azzara rikicin shekarun 2000 mafi muni da kasar ta gani a tarihi da ya mamaye iyakar kasar da Chadi.

Yawan al’ummar da yanzu haka ke zaune a birnin na al-Fashir ya kunshi hadda kusan mutane rabin miliyan da wancan rikici ya tilastawa hijira, lokacin da Sojin kasar suka yi hadaka da dakarun da yanzu suka juye zuwa RSF wajen yakar kungiyoyin ‘yan tawayen da ba na kabilun larabawa ba, sai kuma wasu rabin miliyan da suka sake shiga birnin daga faro rikicin bara.

Tsaffin kungiyoyin ’yan tawayen al-Fashir na ci gaba da taka rawar zama ‘yan baruwanmu duk da yadda RSF ke ci gaba da mamaya bayan kwace garin Melit a watan nan wanda ya kange sojin kasar daga iya isa al-Fashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.