Isa ga babban shafi

Taron birnin Paris ya yi alƙawarin bai wa Sudan tallafin euro sama da biliyan 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce mahalarta taron ƙasa da ƙasa da ya gudana a birnin Paris kan neman tallafa wa al’ummar Sudan da yaƙi ya tagayyara, sun yi alkawarin bayar da euro fiye da biliyan 2.

Wasu daga cikin dubban 'yan Sudan da yaƙin kasar ya raba da muhallansu, yayin da suka samu mafaka a garin Adre da ke Chadi. 16 ga Yuni, 2023.
Wasu daga cikin dubban 'yan Sudan da yaƙin kasar ya raba da muhallansu, yayin da suka samu mafaka a garin Adre da ke Chadi. 16 ga Yuni, 2023. VIA REUTERS - Mohammad Ghannam/MSF
Talla

Faransa da Jamus sun jagoranci taron ne, a daidai lokacin da yaƙin kasar ya cika shekara guda da ɓarkewa a jiya Litinin, 15 ga watan Afrilu.

Ƙazamin rikicin, tsakanin dakarun rundunar RSF da suka yi tawaye a ƙarƙashin jagorancin Muhammad Hamdan Daglo da kuma sojojin gwamnatin shugaba Abdul Fattah al-Burhan, yayi sanadin mutuwar dubban mutanen da har yanzu ba a tattara adadinsu ba a hukumance, yayin da wasu fiye da miliyan 8 suka rasa muhallansu.

Har zuwa wannan lokaci duk wani yuƙuri na taimaka wa miliyoyin mutanen da yaƙin na Sudan ya jefa cikin ƙangin yunwa ya ci tura, sakamakon ƙazamin faɗan da bangarori masu rikici da junan ke cigaba da yi, gami da hana shige da ficen jami’an agaji.

Yanzu haka dai ana fargabar faɗaɗar yakin na Sudan zuwa yankunan ƙasar da a baya bai kai ba, la’akari da yadda faɗan da ake gwabzawa tsakanin sojoji da ‘yan tawayen RSF ya kai kusa da al-Fashir, gari na karshe da har yanzu mayakan basu kame ba a yankin Darfur.

Dubban fararen hula ne dai ke samun mafaka daga tashin hankalin da suka tserewa daga sassan kasar ta Sudan a garin na al-Fashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.