Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 25 na tsananin bukatar agaji a Sudan bayan yakin shekara 1- MDD

Hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai fiye da mutane miliyan 25 da ke tsananin bukatar agaji a Sudan sakamakon yakin kusan shekara guda da kasar ta yi fama da shi, wanda kuma har yanzu babu alamun yiwuwar iya kawo karshensa.

Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023.
Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

A ranar 15 ga watan Aprilun da muke ciki ne yakin na Sudan zai cika shekara guda da farowa dai dai lokacin da yanzu haka kasar da makwabtanta suka shiga halin matsanancin bukatar agaji sakamakon tagayyarar miliyoyin jama’a da ke rayuwa a sansanonin gudun hijira.

Har zuwa yanzu dubban mutane ne ci gaba da ketara iyakar Sudan don samun mafaka a kasashen ketare da nufin gujewa yakin wanda ke ci gaba da lakume rayukan jama’a.

Hukumar ta UNHCR ta ce yakin na Sudan ya raba mutane miliyan 8 da dubu 500 da muhallansu inda miliyan 1 da dubu 800 daga cikin wannan adadi suka tsallaka zuwa kasashen makwabta.

Kakakin hukumar Olga Sarrado akwai akalla ‘yan Sudan dubu 635 da suka tsallaka Sudan ta kudu adadin da ke matsayin kashi 5 na yawan al’ummar kankanuwar kasar mai fama da tashe-tashen hankula baya ga rikicin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.