An gano manyan kaburbura 13 a yankin Darfur - MDD
Ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya samu sahihan rahotannin gano wasu manyan kaburbura akalla 13 a garin El Geneina da ke yankin Darfur da kewayensa a Sudan.
Wallafawa ranar:
Shugaban tawagar jami’an Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Sudan Volker Perthes ne ya bayyana haka, a lokacin da ya gabatar da jawabi kan halin da ake ciki a kasar ga kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya.
Perthes ya ce manyan kaburburan da aka gano suna kunshe ne da wadanda aka kashe yayin hare-haren da dakarun rundunar RSF tare da kawancen wasu mayakan sa-kai larabawa ke kai wa farar hula, wadanda akasarinsu 'yan kabilar Masalit ne.
Jagoran tawagar Majlisar Dinkin Duniyar ya kuma sanar da yin murabus daga mukaminsa a ranar Laraba, matakin da ake kyautata zaton na da alaka da gaza warware rikicin kasar ta Sudan a karkashin jagorancinsa.
Rikicin kabilanci a El Geneina, birnin da ke yammacin Darfur a kusa da kan iyaka da kasar Chadi, ya yi kamari tun bayan yaduwar kazamin rikicin da ya barke tsakanin dakarun RSF da suka bijire da sojojin Sudan a Khartoum babban birnin kasar, a tsakiyar watan Afrilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu