Kotun ICC ta kaddamar da bincike kan kashe-kashen yakin Darfur
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa na gudanar da bincike kan tashe-tashen hankula a yankin Darfur na kasar Sudan. Cikin wannan bincike har da rahotannin kashe-kashe da fyade da kuma laifukan da suka shafi kananan yara, kamar yadda babban mai gabatar da kara ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya a ranar alhamis.
Wallafawa ranar:
Dakarun dake fada da juna na ci gaba da fafatawa a babban birnin kasar Khartoum da kuma wasu yankunan kasar Sudan a rikicin da ya barke a tsakiyar watan Afrilun shekarar nan.
Fiye da mutane miliyan 3 ne suka rasa muhalan su, inda da fiye da 700,000 da suka yi hijira zuwa kasashe makwabta.Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fada a makon da ya gabata cewa, Sudan, kasa ta uku mafi girma a Afirka, na gab da fuskantar yakin basasa da kan iya dagula zaman lafiya a yankin baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu