Isa ga babban shafi
Sudan

Adadin wadanda suka mutu a rikicin kabilanci Darfur ya kai 199

Ma’aikatan lafiya a Sudan sun ce mutane 199 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin kabilancin baya bayan nan da ya tashi a yankin Darfur cikin watanni biyu da suka gabata.

Wasu mazauna yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu, yayin da suke isa sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam dake arewacin Darfur.
Wasu mazauna yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu, yayin da suke isa sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam dake arewacin Darfur. ASSOCIATED PRESS - Sarah El Deeb
Talla

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon takaddama akan mallakar filaye da dabbobi da samar da ruwa da kuma noma, wanda ya kazance tun a farkon watan Oktoban da ya gabata a wasu sassan yankin na Darfur.

Kwamitin Likitoci mai zaman kansa na kasar Sudan ya ce akasarin mutanen da suka mutu harbe su aka yi da bindiga.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM, ta ce tashe-tashen hankulan sun raba mutane fiye da dubu 83,000 da muhallansu.

A shekarar 2003 yakin basasar ya barke a yankin Darfur tsakanin sojojin gwamnati, da 'yan tawayen kabilu marasa rinjaye, wadanda suka yi korafin ana nuna musu wariya, a karkashin gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.