Isa ga babban shafi
Sudan

Adadin wadanda suka mutu a ricikin kabilanci a Darfur ya kai akalla 138

Likitoci a Sudan sunce adadin wadanda da suka mutu sakamakon fadan kabilanci a yankin Darfur ya karu zuwa mutane akalla 138, wasu 106 kuma suka jikkata a cikin makwnni uku da suka gabata.

Wannan hoto da aka dauka 31 ga watan Disamaba ya nuna dubbun 'yan gudun hijira dake kaucewa rikicin yankin Darfur na kasar Sudan.
Wannan hoto da aka dauka 31 ga watan Disamaba ya nuna dubbun 'yan gudun hijira dake kaucewa rikicin yankin Darfur na kasar Sudan. - AFP/File
Talla

Tashin hankalin ya barke ne a ranar 17 ga watan Nuwamba tsakanin Larabawa makiyayan rakuma a tsaunin Jebel Moon na yammacin Darfur.

Cikin adadin mutanen 138 da suka mutun dai har da 25 da aka kashe a ranar Laraba a Jebel Moon.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fadan ya raba mutane sama da 22,000 da muhallansu, yayin da wasu dubu 2000 suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.