Isa ga babban shafi
Sudan

'Yan bindiga sun kaiwa gwamnan yankin Darfur farmaki

Rahotanni daga Sudan sun ce gungun ‘yan bindiga sun yi yunkurin afkawa gidan gwamnan yankin Darfur.

Wasu mazauna yankin Darfur dake gudun hijira a sansanin Kalma.
Wasu mazauna yankin Darfur dake gudun hijira a sansanin Kalma. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Sai dai aniyar 'yan bindigar bata samu ba, sakamakon fatattakarsu da dogaran gwamnan suka yi, bayan fafatawa tsawon sa’a 1.

Babu wanda ya rasa ransa, ko ya samu rauni a harin, zalika maharan basu samu nasarar lalata dukiya ba, yayin farmakin da suka yi yunkurin kaiwa gwamnan na Darfur dake El Geneina, babban birnin yankin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labara kuma babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai farmakin.

Harin dai ya sake tayar da hankulan al’ummar Darfur, inda a makon jiya sama da mutane 200 suka rasa rayukansu a rikicin kabilancin da ya barke, tsakanin Larabawan Rizeigat da kuma ‘yan kabilar Masalit.

Akalla mutane 159 dukkanin bangarorin biyu suka rasa a rikicin, ciki har da mata da kananan yara, zalika rikicin ya tilastawa akalla mutane dubu 90 gudun hijira a makarantu, gine-ginen gwamnati da kuma wasu kauyuka.

Wani lokaci a yau Alhamis kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan halin da sha’anin tsaro ke ciki a yankin na Darfur, inda majalisar ta kawo karshen aikin da dakarunta ke yin a wanzar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.