Isa ga babban shafi
Sudan

Tawagar ICC ta isa Sudan kan bukatar kama masu hannu a rikicin Darfur

Tawagar kotun duniya karkashin jagorancin babbar mai shigar da kararta Fatou Bensouda ta isa birnin Khartoum na Sudan, domin tattaunawa da hukumomin kasar kan sammacin da ta bayar na kama masu hannu a rikicin da ya tagayyar yankin Darfur, cikinsu kuwa har da tsohon shugaba Oumar Al-Bashir.

Tsohon shugaban kasarSudan Umar Hassan al-Bashir a tsare, yayin da ya gurfana gaban kotu a birnin Khartoum.
Tsohon shugaban kasarSudan Umar Hassan al-Bashir a tsare, yayin da ya gurfana gaban kotu a birnin Khartoum. Reuters
Talla

Ana sa ran tawagar kotun duniyar za ta kasance a Sudan har zuwa 21 ga watan Oktoban da muke.

Kotun duniyar ta dade tana neman a kama mata al-Bashir bisa zarge-zargen aikata laifukan kisan kare dangi, da cin zarafin dan adam a rikicin yankin Darfur, da ya barke a shekarar 2003, wanda kuma yayi sanadin mutuwar akalla mutane dubu 300.

Yanzu haka dai tsohon shugaba al-Bashir na tsare a gidan Yarin birnin Khartoum, bayan kifar da gwamnatinsa da sojoji suka yi a watan Afrilun shekarar 2019, biyo bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa da dubban ‘yan Sudan suka shafe makwanni suna yi, kan matsin tattalin arziki da sauran korafe-korafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.