Isa ga babban shafi
Sudan

MDD ta kawo karshen zaman sojojinta a yankin Darfur

Aikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya na wanzar da zaman lafiya a Darfur dake Sudan ya kare a wannan Alhamis 31 ga watan Disamba, a yayin da al’ummar yankin ke cike da fargabar sake barkewar sabon tashin hankali, sakamakon rikice-rikicen kabilancin da suka fuskanta a baya bayan nan.

Wasu kananan yara 'yan Sudan a kusa da motar sulken sojojin Majalisar Dinkin Duniya UNAMID a birnin Nyala, dake yankin Darfur.
Wasu kananan yara 'yan Sudan a kusa da motar sulken sojojin Majalisar Dinkin Duniya UNAMID a birnin Nyala, dake yankin Darfur. AFP
Talla

A shekarar 2003 yaki ya barke a Darfur tsakanin Larabawa da suka mamaye gwamnatin Sudan da kuma mayakan ‘yan tawaye daga kabilu daban daban dake yankin, abinda a wancan lokacin ya sanya gwamnatin Oumar al-Bashir kafa rundunar mayakan Janjaweed da zummar murkushe masu tada kayar bayan.

Akalla mutane dubu 300 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekarun da aka shafe ana gwabza yakin, yayin da wasu miliyan 2 da dubu 500 suka rasa muhallansu, kamar yadda alkaluman majalisar dinkin duniya suka nuna.

Rikicin na Darfur dai yayi sauki matuka a shekarun baya bayan nan, zalika a shekarar bara sojoji suka kawar da gwamnatin shugaba al-Bashir da kotun duniya ICC ke nema bisa tuhumarsa da aikata laifukan yaki a yankin na Darfur dake yammacin Sudan.

Sai dai wasu sun bayyana shakku kan ko gwamnatin rikon kwaryar kasar za ta iya karbar aikin tabbatar da tsaron yankin na Darfur, la’akari da rikice-rikicen kabilancin da har yanzu kan tashi, ciki har da wanda aka kashe mutane 15 a makon jiya, lamarin da ya sanya wasu daruruwan al’ummar yankin gudanar da zanga-zangar adawa da ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.