Isa ga babban shafi
Sudan

Gwamnatin Sudan ta kulla yarjejeniyar sulhu da 'yan tawayen Darfur

An kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da kuma manyan kungiyoyin ‘yan tawayen kasar dake yankin Darfur.

Jami'an gwamnatin Sudan, 'yan tawaye da kuma jami'an diflomasiya bayan kulla yarjejeniyar sulhu da manyan kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur.
Jami'an gwamnatin Sudan, 'yan tawaye da kuma jami'an diflomasiya bayan kulla yarjejeniyar sulhu da manyan kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur. REUTERS/Jok Solomun
Talla

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a ranar asabar ta ta gabata dai za ta kawo karshen yakin basasar da aka share tsawon shekaru 17 ana gwabzawa a yankin.

Sai dai rahotanni sun ce akwai ragowar kungiyoyin ‘yan tawaye 2 da suka ki amincewa da yarjejeniyar Sulhun

Yau Litinin ne kuma ake kyautata zaton bangarorin biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Juba, fadar gwamnatin makociyar kasar wato Sudan ta Kudu, wadda tun cikin shekarar 2019 take taka rawar mai shiga tsakanin kokarin cimma sulhun.

Muhimman batutuwan da yarjejeniyar ta kunsa dai sun hada da, samar da tsaro da kuma hakkin mallakar filaye, raba madafun iko da kuma baiwa jama’ar da suka tserewa yakin na Darfur damar komawa gidajensu.

Majalisar dinkin duniya tace kimanin mutane dubu 300 suka rasa rayukansu a yankin Darfur, bayan barkewar yaki tsakanin ‘yan tawaye da sojin gwamnati daga shekarar 2003 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.