Adadin wadanda suka mutu a rikicin kabilancin Sudan ya zarta 80
Rahotanni daga Sudan na cewa rikicin kabilanci da ake ci gaba da yi a yankin Dafur da ke yammacin kasar ya lakume rayukan mutane 80 ya zuwa yanzu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rikicin da ya barke a ranar Asabar tsakanin ‘yan kabilar Massalit da Larabawa, makiyaya a garin El Geneina ranar Asabar, na zuwa ne makonni 2 kacal bayan da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afrika suka kawo karshen aikin kiyaye zaman lafiya da suka shafe shekaru 13 su na yi a yankin Dafur.
Rikicin ya kazanta, inda kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin suka shiga lamarin, wanda ya kai ga rusa gine gine da gidaje da dama.
A ranar Asabar, Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya tura tawaga mai karfi, ciki har da jami’an tsaro yankin na yammacin Dafur da zummar kawo karshen zub da jinin da ake yi.
A ranar Lahadi jagoran gwamnatin Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya gana da hukumomin tsaron kasar don bin kadin rikicin da ake a yankin na Dafur.
Kungiyar kwararun Sudan, wacce karkashinta aka gudanar da zanga zangar da ta yi sanadin faduwar gwamnatin Omar Al – Bashir a watan Disamban 2018 ta koka da yadda tashin hankalin ya shafi sansanonin ‘yan gudun hijir a yanki.
A ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata ne majalisar dinkin duniya ta kawo karshen aikin kiyayen zaman lafiya da ta ke yi a yankin Dafur bayan shekaru 13.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu