Isa ga babban shafi
Dudan - Darfur

Sudan: Mutane 40 sun mutu a sabon rikicin da ya barke a Darfur

Rahotanni daga kasar Sudan ce akalla mutane 40 suka mutu sakamkon wani rikicin kabilanci a Yankin Darfur dake fama da tashin hankali, yayin da wasu 54 suka jikkata a garin El Geneina.

Wasu mazauna yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu, yayin da suke isa sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam dake arewacin Darfur.
Wasu mazauna yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu, yayin da suke isa sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam dake arewacin Darfur. ASSOCIATED PRESS - Sarah El Deeb
Talla

Bayanai sun ce an gwabza fadan ne a karshen makon da ya gabata a garin dake kusa da iyakar Chadi, kuma har zuwa jiya da Safiya ana jin amon bindigogi na tashi, yayin da ake hango hayaki.

Kungiyar likitocin Yankin tace ta karbi gawarwaki 18 da marasa lafiya 54 wadanda ke karbar magani a asibitin koyarwar El Geneinan.

Babu bayani kan abinda ya haddasa tashin hankalin.

Wasu mata da rikici ya raba da muhallansu a wani sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Darfur.
Wasu mata da rikici ya raba da muhallansu a wani sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Darfur. ASSOCIATED PRESS - Nasser Nasser

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamman mutane ke rasa rayukansu sakamakon barkewar rikici a yankin El Geneinan dake yankin Darfur a Sudan ba, inda a farkon wannan shekara rikicin kabilanci lakume rayukan mutane kusan 80.

 

Rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Massalit da Larabawa, makiyaya a garin El Geneina na zuwa ne makwanni 2 kacal bayan da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afrika suka kawo karshen aikin kiyaye zaman lafiya da suka shafe shekaru 13 su na yi a yankin Dafur.

A ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata ne majalisar dinkin duniya ta kawo karshen aikin kiyayen zaman lafiya da ta ke yi a yankin Dafur bayan shekaru 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.