Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan: An gano sabbin kaburbura a yankin Darfur

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, an gano gawarwakin mutane da dama da ake zargin dakarun sa-kai na Sudan da kawayenta ne suka kashe a wani kabari da ke yammacin Darfur.

Daya daga cikin manyan kaburburan da aka rika ganowa a yankunan da suka taba kasancewa a karkashin ikon mayakan ISIS a Libya.
Daya daga cikin manyan kaburburan da aka rika ganowa a yankunan da suka taba kasancewa a karkashin ikon mayakan ISIS a Libya. © REUTERS/Ayman Al-Sahili
Talla

A cewar rahoton da ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya samu, an jibge gawarwakin mutane 87, wadanda wasu daga cikinsu 'yan kabilar Masalit 'yan kabilar ne a wani kabari mai tsawon mita daya daura da birnin Geneina na yammacin Darfur.

A ranar 20 ga watan Yuni ne aka binne gawarwakin mutane 37 na farko, kamar yadda hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a cikin wata sanarwa daga Geneva.

Rahoton ya ci gaba da cewa, an binne wasu gawarwaki 50 a wuri guda ranar 21 ga watan na Yuni, ciki kuwa akwai mata bakwai da yara bakwai.

Yankin Darfur dai ya kasance cibiyar rikicin na tsawon makonni 12, inda ya rikide zuwa rikicin kabilanci inda dakarun RSF da mayakan sa-kai na Larabawa ke kai hare-hare kan kabilun Afrika.

Labarin binne tarin gawawwakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta gudanar da bincike kan ta'asar da ake yi a yankin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.