Isa ga babban shafi

Yakin Sudan ya raba mutane miliyan 7 da muhallansu

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayanan da ke cewa sama da mutum miliyan 7 ne suka tsere daga muhallansu dalilin yakin da ke ci gaba da tsananta a Sudan.

Біженці із Західного Дарфуру у Чаді, липень 2023
Wasu da yaki ya rabasu da muhallansu a Sudan. © Zohra Bensembra / Reuters
Talla

Mai magana da yawon babban sakataren Majalisan Dinkin Duniya Stephane Dujarric, ya ce alkaluman hukumar kula da kaurar baki ta IOM sun nuna yadda mutanen da yawansu ya kai dubu dari uku suka bar yankin Wad Madani da ke jihar Al-Jazira sakamakon tsanantar yakin na Sudan.

Dujarric ya kara da cewa, mutum miliyan daya da rabi ne suka gudu daga Sudan zuwa ketare, wannan ne ya sa aka samu mutum miliyan bakwai da dubu dari daya da suka gudu daga matsugunan, alkaluman da ke mayar da Sudan kasar da ke da mafi yawan mutanen da suka tsere daga mahallan su sakamakon yaki a duniya.

Sama da mutane dubu dari biyar ne suka tsere zuwa Al-jazira, inda nan ne ya kasance wuri mafi zaman lafiya a kasar kafin daga bisani yakin ya ci birnin Wad Madani fadar gwamnatin jihar.

Mutane da yawa sun bayyana bakin cikin su da suke ganin cewa, sun gujewa tashin hankali daga Khartoum zuwa Wad Madani, sai dai kuma shi ma birnin ya fara fuszkantar wannan iftila’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.