Isa ga babban shafi

Yakin Sudan ya juye rikicin kabilanci a yankin yammacin Darfur- MDD

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren mayakan RSF ya hallaka daruruwan fararen hula a yankin Yammacin Darfur na Sudan baya ga tilastawa wasu dubbai tserewa daga matsugunansu don kaucewa hare-haren.

Wasu da rikici ya raba da muhallansu a yankin yammacin Darfur na Sudan.
Wasu da rikici ya raba da muhallansu a yankin yammacin Darfur na Sudan. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Hare-haren na RSF da hadin gwiwar kungiyoyin tsageru masu rike da makamai a yankin na yammacin Darfur da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana a matsayin na kabilanci, a cewar hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar shi ne mafi munin zubda jini da yankin ke gani a baya-bayan nan wanda ya tsananta tun bayan barkewar yakin kasar a watan Aprilu.

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Volker Turk ya ce dakarun RSF da hadin gwiwar mayakan kungiyoyin larabawa masu rike da makamai sun kashe daruruwan fararen hular da suka fito daga kabilun da ba na larabawa ba musamman kabilar Masalit.

A cewar Turk wannan hare-hare na kabilanci na kokarin dawo da mafi munin rikicin kabilanci da yankin ya yi fama da shi a shekarun 2003 da 2008 lokacin da aka kashe fararen hular da yawansu ya kai dubu 300, batun da jami’in ke cewa ba a fatan sake fuskantar makamancinsa.

Shugaban na hukumar kare hakkin dan adam ya bayyana cewa hari na baya-bayan nan kan fararen hular shi ne wanda aka kai kan birnin Geneina fadar gwamnatin yankin na Yammacin Darfur tare da kashe tarin fararen hular da basu ji basu gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.