Isa ga babban shafi

EU na shirin lafta takunkumai kan masu hannu a rikicin Sudan

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da matakin lafta takunkumai kan jagororin Sudan wadanda ke da hannu a rikicin kasar wanda ke ci gaba da tsananta, duk da kokarin shiga tsakanin kasashe na shawo kan sa.

Matsalar tsaro na ci gaba da tsananta a sassan Sudan musamman jihar Port Sudan.
Matsalar tsaro na ci gaba da tsananta a sassan Sudan musamman jihar Port Sudan. REUTERS - IBRAHIM MOHAMMED ISHAK
Talla

Tun cikin watan Yulin da ya gabata ne, wasu kasashe mambobin EU suka shigar da kudirin ganin kungiyar ta amince da lafta takunkumai kan jagororin na Sudan wadanda suka yi tsayuwar gwamen jaki duk da yunkurin kasashe na ganin an shawo kan rikicin kasar ta Afrika da ke ci gaba da lakume dimbin rayukan fararen hula, amma sai a farkon makon nan ne, majalisar ta EU ta amince da kudirin.

Wata majiya makusanciya ga kungiyar ta EU ta ce takunkuman sun kunshi rufe dukkanin asusun ajiyar jagororin da ke kasashen baya ga haramcin tafiya-tafiye, ko da ya ke sai a karshen watan nan ne ministocin wajen kasashen kungiyar za su kamma sanya hannun amincewa da takunkuman.

Tun a ranar 15 ga watan Aprilun shekarar nan ne rikici ya barke tsakanin jagoran mulkin Sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kai daukin gaggawa na RSF wato Mohamed Hamdan Dagalo, rikicin da hukumar kula da kaurar baki ta duniya ke cewa ya raba iyalai fiye da miliyan 4 da muhallansu a sassan kasar yayinda wasu fiye da miliyan guda ke hijira a ketare.

Dakarun Sojin Sudan a ci gaba da yakin da suke da mayakan RSF.
Dakarun Sojin Sudan a ci gaba da yakin da suke da mayakan RSF. © AFP

Ko a watan jiya, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin fadawar miliyoyin mutane matsanancin halin yunwa a sassan Sudan sakamakon karancin abincin da kasar ke fuskanta mai nasaba da rikicin.

Bangarori daban-daban da suka kunshi Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa dama manyan kasashe sun yi yunkurin shiga tsakani don sasanta rikicin tsakanin jagororin Sojin na Sudan biyu amma lamarin ya ci tura, batun da ke cikin hujjojin da EU ta yi amfani da su wajen lafta takunkuman.

Takunkuman na EU na zuwa bayan makamantansu daga Amurka, wadda tun farko fara yakin ta sanya takunkumai kan jagororin wadanda ta ce basu da niyyar kawo karshen yakin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.