Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Kiir ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhun Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu a ranar Laraba domin kawo karshen rikicin kasar tsakanin shi da ‘Yan tawaye da suka shafe watanni 20 suna gwabza fada da juna.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir AFP PHOTO/ CHARLES LOMODONG
Talla

Tuni dai shugaban ‘Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar ya sanya hannu kan yarjejeniyar.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun bukaci gwamnatin Sudan ta Kudu ta mutunta illahirin sharuddan da ke kunshe a yarjejeniyar sulhun da ta sanya wa hannu tsakaninta da ‘yan tawaye.

Amurka ta gargadi Salva Kiir kan gujewa abin da zai iya haifar da matsala a yarjejeniyar da aka kulla.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka na fatar wannan matakin zai taimaka wajen kawo karshen rikicin kasar da aka shafe watanni 20 ana gwabzawa.

Sanya hannun da shugaba Salva Kiir ya yi kan yarjejeniyar na zuwa ne bayan ya dade yana jan kafa a kai, tare da bayyana shakkun ingancinta.

An dade bangarorin da ke rikici a Sudan ta kudu na karya yarjejeniyar tsagaota wuta da suka amince kusan guda bakwai.

Dubun dubatar mutane ne dai suka mutu a rikicin Sudan ta kudu tare da tursasawa daruruwa gujewa gidajensu.

Shugabannin Kasashen Afrika 8 na kungiyar IGAD ne suka jagoranci amincewa da yarjejeniyar tare da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika da China da Birtaniya da Norway da kuma Amurka.

Karkashin yarjejeniyar dai, Reik Machar kwamandan ‘Yan tawaye zai iya komawa kan mukaminsa na Mataimakin shugaban kasa bayan tube shi a watan Yulin 2013, lamarin da ya jefa Sudan ta kudun cikin rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.