Isa ga babban shafi

Kasashen Afrika sun dakile amfani nau'in gurbataccen maganin tarin yara - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce babu sauran nau’in gurbataccen maganin tarin kananan yara samfurin Benylin a sassan kasashen Afrika, yankin da aka shafe lokaci ana sayar da maganin ya kuma haddasa mace-macen tarin yara a kasashe daban-daban.

Wasu nau'ikan gurbatattun magungunan tari da suka kashe tarin kananan yara a Gambia.
Wasu nau'ikan gurbatattun magungunan tari da suka kashe tarin kananan yara a Gambia. AFP - MILAN BERCKMANS
Talla

Galibin kasashen Afrika irinsu Kenya da Rwanda da Tanzania da Zimbabwe baya ga ita kanta Afrika ta kudu da ke samar da nu’in maganin na Benylin sun dauki matakan dakile amfani da shi ta hanyar kawar da shi daga kasuwa.

Haka zalika ko cikin watan nan sai da Najeriya ta janye nau’in gurbataccen maganin daga kasuwanni sakamakon yadda gwaji ya bankado ya na dauke da sinadarin diethylene mai tarin yawa da ke da hadari ga kodar kananan yara.

A cikin watan Mayun shekarar 2021 ne nau’in maganin na Benylin da reshen kamfanin Johnson and Johnson na Afrika ta kudu ya samar ya fara gamuwa da tangarda ko da ya ke tuni kamfanin Kenvue ya karbi ragamar samar da nau'in maganin a bara.

Wani sakon yanar gizo da J&J ya aikewa Kenvue a juma’ar da ta gabata, ya bukaci karin bayani kan ikirarin samun sinadaran na ko dai diethylene ko kuma ethylene glycol a cikin maganin, wanda Kenvue ke cewa bincikensa bai gano zargin da mahukunta Najeriya suka yi maganin ba, sai dai suna ci gaba da aiki tare don gano hakikanin gaskiyar lamarin.

Sinadarin Diethylene glycol da ke haddasa ciwon koda, samunsa a wani nau’in maganin tarin yara wanda India da Indonesia ke samarwa ya haddasa mutuwar kananan yara fiye da 300 a kasashen Kamaru da Gambia da Indonesia da kuma Uzbekistan tun daga shekarar 2022 kawo yanzu.

Sai dai har zuwa yanzu babu rahoton mutuwa ko kuma haddasa wata mummunar illa bayan amfani da nau’in maganin na Benylin samfurin Afrika ta kudu, duk da cewa WHO na duba yiwuwar daukar matakan haramta amfani da nau’in maganin, bayan da hukumar ta bukaci kasashe su sanya idanu don dakile bazuwarsa a kasuwanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.