Isa ga babban shafi
MDD-SUDAN-KUDU

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi mayaka a Sudan ta Kudu kan karya yarjejeniya

Komitin tsaro na MDD ya bukaci tsagaita buda wuta mai dorewa kuma nan take, a kasar Soudan ta Kudu, tare da gargadin daukar matakan ladabtarwa a kan duk wanda ya karya yarjejeniyar da aka sakawa hannu tsakanin bangarorin dake fada da juna a kasar.

An cimma ranke-ranken yarjejeniyar zaman lafiya a sudan ta kudu tsakanin Rik Machar da shugaba Salva Kiir
An cimma ranke-ranken yarjejeniyar zaman lafiya a sudan ta kudu tsakanin Rik Machar da shugaba Salva Kiir REUTERS/Jok Solomun
Talla

A cikin wata sanarwa da daukacin mambobin kwamitin tsaro na MDD 15 suka sakawa hannu, sun yabawa abukan gabar 2 a kasar ta Sudan ta kudu da suka saka hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wutar, shugaban kasar Salva Kiir da kuma Riek Machar tsohon mataimakin shugaban kasar da ya zama dan tawaye, inda suka bukace su da su mutunta daukacin bangarorin yarjejeniyar da aka cimma.

Sama da mutane dubu 10 ne aka kashe a cikin fadan basasar da ya goce watanni 20 da suka gabata a kasar ta Sudan ta Kudu, jinjirar kasa mai arzikin man Fetur dake yankin tsakiyar Afrika, shekaru 3 bayan samun yancin kanta daga kasar Soudan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.