Isa ga babban shafi

An sako wasu mutane da aka yi garkuwa da su a kusa da Bandiagara na kasar Mali

A kasar Mali ,fiye da fasinjoji dari a cikin motocin bas guda uku da ke tafiya tsakanin Bankass da Bandiagara, a tsakiyar kasar ne,  wasu mutane dauke da makamai suke tsare da su,maharan da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi karkashin kungiyar Jnim (Kungiyar da ke ikirarin tallafawa Musulunci da Musulmai), karkashin inuwar al-Qaeda ne.Wasu rahotanni na bayyana cewa an sako wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Mutanen kauyen Bandiagara
Mutanen kauyen Bandiagara © Club RFI Bandiagara
Talla

An saki mutane goma sha biyu, yayin da maharan ke ci gaba da tsare da dama daga cikin fasinjojin ,babu sahihin alkaluma  dangane da adadain mutanen da wadanan ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su duk da cewa lokacin da abin ya faru ranar kasuwar yankin ne.

A lokacin da wannan al’amari ya faru,ba a samu tabacin faruwar lamarin ba,sai dai majiyoyin gida da dama da RFI ta tuntuba sun danganta maharan da na kungiyar  Katiba Macina na Jnim, wanda suka dau nauyin sace mutane da dama a baya.

Wasu daga cikin matasa bakin rijiya a yankin Bandiagara na kasar Mali
Wasu daga cikin matasa bakin rijiya a yankin Bandiagara na kasar Mali AFP - FRANCOIS XAVIER MARIT

A tsakiyar kasar Mali, a cikin 'yan shekarun nan, al'ummar gundumomi da dama sun amince da mika wuya ga dokokin kungiyoyi masu da’awar jihadi,mutanen yankuna da dama sun cimma yarjejeniya na biyan su haraji, da amincewa da wasu dokokin  da suka jibanci zamantakewa da al’adu na yau da kullum da kuma dorewa a hakan,hanya daya ko mafita ga mutanen yankunan samun damar tafiya cikin walwala da ci gaba da ayyukan noma.

Gine-ginen gargajiya a garin Bandiagara na kabilar Dogon dake yankin tsakiya Mali
Gine-ginen gargajiya a garin Bandiagara na kabilar Dogon dake yankin tsakiya Mali AFP / FRANCOIS XAVIER MARIT

Wadanda aka yi garkuwa da su ne suka fito daga kananan hukumomin da ba su kulla yarjejeniyoyin cikin gida da kungiyoyin ba wadanda har yanzu ake tsare da su ba.

A cikin 'yan kwanakin nan, an shirya zanga-zanga a yankuna da dama na yankin domin neman mahukuntan rikon kwarya da su kara kaimi, domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.