Sai an daidaita yanayin tsaro gaba daya kafin a je zaben kasar Mali - Choguel
Firaministan kasar Mali Choguel Kokalla Maiga ya na mai bayyana cewa 'Gwamnatin mulkin sojin kasar za ta shirya zabuka ne kawai domin mika mulki ga farar hula da zarar an daidaita yanayin tsaro gaba daya.Mali na karkashin mulkin sojoji ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan a shekarar 2020 da 2021, inda matsalar tsaro ke kara ta'azzara daga kungiyoyin masu ikirarin da suka kama wasu yankunan kasar.
Wallafawa ranar:
Firaminista Choguel Kokalla Maiga ya ce, "Dole ne matakin tabbatar da zaman lafiya ya kai matsayin da ba za a sake komawa gidan jiya ba, matakin da ya dace da samun damar shirya zabuka a wannan kasa.
Choguel Kokalla Maiga na Magana ne a gidan talabijin na kasar da kuma aka watsa a kafofin sada zumunta da yammacin ranar Alhamis. .
Choguel Kokalla Maiga ne babban jami'i na farko da ya kawo Karin haske kusan kwana daya da yan siysa suka soma bayyana damuwa yan lokuta da majalisar sojin ta sanar da haramta ayyukan jam’iyyun siyasa a kasar ta Mali. Majalisar sojin kasar ta dau alkawalin mika mulki idan wa’din ya cika,sai ga shi ta kasa cika wannan alakwari na ranar 26 ga Maris, 2024.
Sakamakon matsin lamba daga kungiyar ECOWAS a yankin, gwamnatin mulkin soji kasar Mali ta yi alkawarin shirya zaben shugaban kasa a watan Fabrairu tare da mika mulki a karshen watan Maris, amma ta janyo suka a cikin gida bayan ta kasa yin hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu