Isa ga babban shafi

Sojin Mali sun haramta tarukan siyasa duk da gaza cika alkawarin gudanar da zabe

Gwamnatin Mali ta zartas da wata dokar Soji ta gaggawa da ta haramta duk wasu taruka ko kuma gangamin jam'iyyun  siyasa a wani yunkuri na kange kiraye-kirayen da suke na ganin mahukuntan kasar ta yammacin Afrika sun kira zabe don komawa karkashin mulkin demokradiyya.

Shugaban gwamnatin Sojin Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin Sojin Mali Kanal Assimi Goita. AFP/File
Talla

Matakin Sojin na Mali na zuwa ne a dai dai lokacin da kiraye-kiraye ke ci gaba da karfi daga ciki da wajen kasar don ganin an gudanar da zabe kamar yadda gwamnatin Sojin ta yi alkawari a baya.

Sanarwar da kakakin gwamnatin ta Mali Abdoulaye Maiga ya karanta a gidan talabijin mallakin gwamnati da yammacin jiya Laraba, ya ce matakin haramta dukkanin lamurran jam’iyyun siyasan na da nasaba da yunkurin da gwamnati ke yi na tabbatar da doka da oda.

Sanarwar ba ta fayyace barazanar da ta ikirarin tarukan jam’iyyun nsiyasar ka iya haifarwa al’ummar kasa ba, sai dai ta ce za ta haramta duk wani yunkurin haifar da tarzoma tsakanin jama’a.

Babu dai hakikanin lokacin da gwamnatin ta Mali za ta sanar da dage wannan haramci kan jam’iyyun siyasa wadanda a baya-bayan nan suka tsananta kiraye-kiraye wajen ganin kasar ta koma turbar demokradiyyar ta hanyar zaben halastaccen shugaba.

Tun a shekarar 2020 ne Sojoji suka fara mulki a Mali bayan hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, kuma a watan Disamban bara gwamnatin Sojin ta jaddada shirin gudanar da zabe a watan Fabarairun shekarar nan, amma ba tare da nasarar iya gudanarwar ba.

Mali dai har zuwa yanzu ba ta sanar da sabon lokacin zabe bayan karewar wa’adin da aka dibarwa lokacin gwamnatin rikon kwarya tun a watan Maris din da ya gabata.

Wannan dalili ya sanya kiraye-kiraye daga bangaren kungiyoyin fararen hula da jam’iyyun siyasa, lamarin da ya haddasa wannan doka da ta haramta duk wasu taruka ko gangamin jam’iyyun siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.