Isa ga babban shafi

Hare-haren masu dauke da makamai na kara kamari a kasashen Nijar da Mali

Hare-haren masu tayar da kayar baya na ci gaba da karuwa a kasashen Nijar da Mali, inda shugabannin mulkin sojan kasashen ke da muradin ci gaba da mulki, yayin da masana tsaro ke bayyyana fargabar cewa zabukan da ke tafe a yankin Sahel da alama na cikin tsaka mai wuya.

Tutar Nijar da Najeriya kenan da ke kadawa a sansanin sojin Amurka da ke Agadez, Nijar.
Tutar Nijar da Najeriya kenan da ke kadawa a sansanin sojin Amurka da ke Agadez, Nijar. AP - Carley Petesch
Talla

Dukkanin kasashen dai sun amince cewa kalubalen da ake fuskanta a yankin ya fi yadda ake zato, a cewar Afolabi Adekaiyaoja, wani manazarcin siyasa a cibiyar ci gaban dimokuradiyya a Abujan Najeriya ga RFI.

Ya kara da cewa tashe-tashen hankulan na faruwa ne sakamakon yawaitar kungiyoyin masu dauke da makamai.

A farkon wannan shekarar ne kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka bayyana aniyarsu ta ficewa daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka tare da kafa wata sabuwar kungiya mai suna kawancen kasashen yankin Sahel.

Masana na ganin cewa, ficewar sojojin kasashen yammacin duniya a wadannan kasashe, ya bayar da  mamaki, musamman a Nijar.

A kasar Mali, ya kamata a yi amfani da taswirar da za ta kai ga gudanar da zabe a cikin watan Fabrairu, amma tuni shugabannin sojin kasar suka gaza cika wa'adin.

Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da IS sun kaddamar da hare-hare a yankin Tillaberi na Nijar da ke kan iyaka da Mali, Burkina Faso da Benin, tun a shekarar 2017, duk da dimbin dakarun da ke yaki da masu dauke da makamai.

A Mali, dakarun da ke dauke da makamai da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen waje irin su Wagner ta Rasha, sun kashe fararen hula da dama ba bisa ka’ida, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.