Isa ga babban shafi
ECOWAS

Najeriya za ta kashe dala miliyan 100 kan yakar ta'addanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi alkawarin bada gudunmawar dala miliyan 100, domin yakar ta’addanci a kasashen Afrika ta yamma.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@MBuhari
Talla

Buhari ya bayyana haka ne ta hannun ministan harkokin wajensa Mista Geoffery Onyeama, yayin taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDAO da aka soma shi a jiya Asabar ta kafar bidiyo.

Shugaban ya ce a kashin Najeriya za ta mikawa ECOWAS dala miliyan 20, don taimaka mata wajen yakar ta’addanci, yayin da kuma za ta yi amfani da dala miliyan 80 wajen murkushe ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram a yankunan arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashin kasar.

Taron shugabannin kasashen na ECOWAS kashi na 58 ya maida hankali ne kan tsaro, tattalin arziki, da kuma lamurran siyasar da suka shafi kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.