Isa ga babban shafi

Najeriya da Nijar sun zuba jarin dala miliyan 100 don bunkasa harkokin noma a yankin Sahel

Kasashen Najeriya da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun yi hadaka wajen zuba jarin dala miliyan 100 don bunkasa harkokin noma da samar da abinci a yankin Sahel.

Map of Nigeria, Mali and Niger
Map of Nigeria, Mali and Niger RFI
Talla

Daraktan shirye-shirye na cibiyar habaka samar da taki ta kasa da kasa Bidjokazo ya ce hadakar kasashen 4 na Najeriya da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar na da nufin yakar kwararowar hamada da kuma inganta kasar shuka don wadata yankin Sahel da abinci.

Wannan hadaka na zuwa a dai dai lokacin da matsaloli masu alaka da zaizayewar kasa da bushewar gonaki baya ga karancin zubar ruwan sama ke barazana ga harkokin noman kasashen dama halittun da ke rayuwa a ruwa sakamakon yadda tafkuna ke ci gaba da kafewa.

Tun a shekarar 2023 dama hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane akalla miliyan 26 da dubu 500 za su fuskanci kamfar abinci a Najeriya tsakanin watan Yuni zuwa Agustan bana.

A cewar hukumar ta FAO wanna lamari zai fi tsananta a jihohin Borno da Sokoto da kuma  Zamfara har ma da Abuja fadar gwamnatin kasar.

A cewar Fofana Najeriya ce kan gaba a yawan kudin da aka zuba a hadakar da dala miliyan 40 yayin da sauran kasashen 3 na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso kowaccensu ta zuba dala miliyan 20.

Babban jami’in na kasa da kasa ya bayyana cewa shigar Najeriya shirin ko shakka babu zai taimakwa wajen magance matsalolin na Sahel ta fuskar noma, lura da yadda matsalar ke ci gaba da tsauwala yanayin rayuwa ga al’ummar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.