Isa ga babban shafi

An fara aikin rijistar ‘yan Nijar kusan 120,000 na kasashen waje

A ranar asabar 15 ga watan Oktoban nan  ne hukumar zabe mai zaman kanta a jamhuriyar Nijar ta kaddamar da shirin tantance ‘yan kasar Nijar a kasashen waje tare da mambobi kusan 118.000.

Zakari Oumarou shugaban tawagar gwamnatin Nijar da ta iso Najeriya a shirin itattance yan Nijar a Najeriya
Zakari Oumarou shugaban tawagar gwamnatin Nijar da ta iso Najeriya a shirin itattance yan Nijar a Najeriya © ©Rfi
Talla

An aike da jami’an hukumar a kasashe 15 da aka zaba bisa ga adadin yan Nijar, kasancewar wakilan diflomasiyya ko na ofishin jakadancin, amma kuma la'akari da yanayin tsaro.

Kasashen da za a gudanar da wannan aiki sun hada da : Algeria, Benin, Kamaru, Cote D’Ivoire, Ghana, Mali, Najeriya, Morocco, Senegal, Chadi, Togo, Belgium, Faransa da Amurka.

Za a share makonni biyu, ana gudanar da wannan aiki a wadanan kasashe.

A karshen ayyukan kidayar yan Nijar mazauna kasashen waje a karshen shekarar nan ta  2022, kwata na farko na shekarar 2023, za a gayyace mutanen da aka yiwa rijista  zuwa zaben ‘yan majalisar dokoki na wani bangare don cike kujeru 5 na yan majalisun.

 Majalisar dokokin Nijar ta kumshi wakilai 171.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.