Isa ga babban shafi

'Yan Nijar sun bukaci ficewar sojojin Faransa daga kasarsu

Daruruwan 'yan Nijar ne yau suka shiga zanga zangar lumana a birnin Yammai domin bukatar janyewar dakarun Faransa dake yaki da 'yan ta’adda da ake kira Barkhane daga kasar.

Wasu daga cikin tawagar dakarun barkhane kenan
Wasu daga cikin tawagar dakarun barkhane kenan © Franck Alexandre / RFI
Talla

Masu zanga zangar sun yi ta shelar bayyana bukatar janyewar dakarun da kuma jinjinawa shugaban Rasha Vladimir Putin lokacin da suka yi tattaki zuwa gaban Majalisar dokokin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar wasu daga cikin masu zanga zangar suna dauke da tutar kasar Rasha, tare da kuma rubuce rubucen dake sukar Faransa da Rundunar Barkhane.

Wasu daga cikin allunan na bayyana bukatar ficewar sojojin Faransar, yayin da suke bayyana cewar duk da zaman su a Nijar, ana ci gaba da kai hare hare ana kashe mutane.

AFP yace akwai akalla sojojin Faransa 3,000 a Yankin sahel, kuma wasu daga cikin su na Jamhuriyar Nijar, bayan janye su daga kasar Mali.

A watan Afrilun da ta gabata, 'yan majalisun Nijar sun kada kuri’ar amincewa da bukatar girke sojojin Faransa a kasar domin taimaka mata yaki da 'yan ta’adda.

Seydou Abdoulaye, daya daga cikin shugabannin kungiyar M62 da suka shirya zanga zangar ya shaidawa AFP cewar, suna nuna kyamar ci gaba da zaman sojojin Barkhane dake Nijar, saboda haka suke bukatar ficewar su.

Abdoulaye dake sanye da rigar dake dauke da hotan tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore, ya zargi Faransa da taimakawa 'yan ta’adda wajen yada ayyukan ta’addanci a Mali dake makotaka da Nijar da kuma Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.