Isa ga babban shafi

kungiyar Amnnesty International ta yi kira ga hukumomin Nijar da su kyautata rayuwar fursunoni

A jamhuriyar Nijar kungiyar kare hakin jama'a ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kira ga hukumomin kasar da su dau matakai domin kyautata rayuwar fursunonin gidan yarin kutukale ta fannin kula da lafiya da abincinsu.

Gidan yarin Koutoukalé a Jamhuriyar Nijar
Gidan yarin Koutoukalé a Jamhuriyar Nijar BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Kungiyar ta ce fursunonin na fama da kuncin rayuwa,lamarin da ya sabawa dokokin kula da fursunonin na duniya.

Sakamakon bincike daga wasu daga cikin kungiyoyin masu kare hakokkin bil Adam a Nijar sun bayyana matukar damuwa,inda wasu iyalan mutane da ake tsare da su ,tsawon shekaru ba a basu damar saduwa da yan uwan su da ake tsare da su a kurkuku.

Gidan yarin  Koutoukalé, a Jamhuriyar Nijar
Gidan yarin Koutoukalé, a Jamhuriyar Nijar RFI/Moussa Kaka

Da jimawa hukumomin na Nijar na fadar cewa kare hakokkin bil Adam na daga cikin manyan ayukan da suka saka gaba,yayinda rahotanni daga wadanan kungiyoyi na  nuna sauyi a kai.

Baro Arzika wakilin mu daga birnin Yameh ya duba mana labarin ,ga kuma rahoto da ya hada mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.