Nijar ta fara shirye-shiryen neman sulhu da 'yan ta'adda
Jamhuriyar Nijar na shirin tattaunawa da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, wadanda hare haren da suke kaiwa a kudu maso yammacin kasar suka girgiza ta.
Wallafawa ranar:
Kasar da ke yankin Sahel na fargabar yadda ‘yan ta’addan suka sabanta hare hare a yankin Tillaberi tun bayan da Faransa ta sanar da cewa dakarunta za su bar kasar Mali.
Wata majiya daga ofishin shugaba Bazoum Mohamed ta ce a watanni uku da suka wuce ne dai shugaban kasar ya tuntubi matasa da kungiyar IS ta yammacin Afrika ta dauka aiki a game da batun sulhu.
Majiyar ta ce shugaba Bazoum ya aike da manzanni don ganawa da wasu shugabannin ‘yan ta’adda 9.
A ‘yan kwanakin da suka wuce ne dai shugaba Bazoum ya saki ‘yan ta’adda da dama daga gidan yari, har ma ya karbi bakuncinsu a fadar gwamnatin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu