Shugaban Nijar ya ziyarci kamfanin samar da makamai na Turkiya
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya kai ziyara kamfanin samar da makamai dake kasar Turkiya da zummar samar da sojojin kasar karin kayan aikin da zasu shawo kan matsalolin tsaron da suka addabe su.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni sun ce shugaban ya ziyarci kamfanin Baykar dake samar da na’urorin liken asiri da kuma na kai hare hare tare da jiragen sama masu sarrafa kan su domin inganta yaki da ta’addancin da kasar keyi.
Sanarwar fadar shugaban tace ana saran gabatarwa kasar da wadannan sabbin makamai cikin ‘yan watanni masu zuwa domin fara amfani da su.
Daga cikin Yan tawagar shugaban harda ministocin tsaro da harkokin waje da na fadar shugaban kasa da kuma Babban Hafsan tsaron sojin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu