Isa ga babban shafi
Nijar-Ta'addanci

Nijar ta saki jagororin 'yan ta'adda daga yari a kokarin dawo da zaman lafiya

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun sanar da sakin wasu shugabannin ‘yan ta’adda ciki har da jagororin kungiyar Boko Haram a wani yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar ta yammacin Afrika mai fama da hare-haren ta’addanci.

Shugaba Bazoum Mohammed na jamhuriyar Nijar.
Shugaba Bazoum Mohammed na jamhuriyar Nijar. © Niger Presidency
Talla

Tun a jiya juma’a shugaba Bazoum Mohamed ya sanar da matakin sakin jagororin ‘yan ta’addan yayin wani taro kan harkokin tsaro da ya jagoranta tare da manyan hafsoshin tsaron kasar da jami’an gwamnati da masu rike da sarautun gargajiya.

Acewar Bazoum masana tsaro sun shawarce shi da ya sakin jagororin ‘yan ta’addan 9 da ke tsare tsawon lokaci a gidan yari don tabbatar da zaman lafiyar Nijar.

Gidajen talabijin din Nijar sun ruwaito shugaba Bazoum na cewa manufarsa shi ne tabbatar da zaman lafiyar al’ummar Nijar.

Kafin bayyanarsu a fadar shugaban kasa, manyan jagororin ‘yan ta’addan 9 na tsare ne a gidan yarin Koutoukale mai tsauraran matakan tsaro da ke kudancin garin Kollo.

Wata sanarwar fadar shugaban kasa ta ce sakin adadin jagororin ‘yan ta’addan shi ne irinsa na farko da gwamnatin Nijar ta gudanar a yunkurinta na laluben hanyoyin dawo da zaman lafiya a kasar.

Nijar wadda ke sahun matalautan kasashe na fama da hare-haren ta’addancin mayaka masu ikirarin jihadi ne da ke tsallakowa kasar daga Mali da kuma Boko Haram daga Najeriya.

Zuwa yanzu a cewa shugaba Bazoum Mohamed akwai dakarun Nijar dubu 12 da ke fagen daga wajen yaki da mayakan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.