Isa ga babban shafi
Nijar

Amnesty ta bayyana damuwa kan makomar aikin Jarida a Nijar

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta bayyana fargaba a game da makomar ‘yancin aikin jarida a Jamhuriyar Nijar, bayan da kotu ta yanke hukuncin daurin talala a kan wasu ‘yan jaridu biyu saboda sake wallafa labarin da wata jarida ta wallafa dangane da matsalar fataucin miyagun kwayoyi a kasar.

Wasu 'yan Jarida a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
Wasu 'yan Jarida a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar © Issofou Sanogo/AFP/Getty Images
Talla

A ranar 3 ga wannan wata na Janairu ne kotu a Yamai ta yanke hukuncin daurin talala a kan Samira Sabou da Moussa Aksar saboda sun sake wallafa labaran da wata Cibiya da ke Geneva mai suna Global Initiative Against Transnational Organized Crime (GITOC) ta buga, da ke cewa mahukunta a kasar ta Nijar, sun sake mika miyagun kwayoyin da jami’an tsaro suka kwace daga hannun wasu fatake.

Ma’aikatar shari’a ta yi amfani da dokar da ke hukunta masu aikata laifi ta yanar gizo ne domin daure ‘yan jaridar biyu, hukuncin da Ousman Diallo, mai bincike a ofishin kungiyar ta Amnesty na Yammacin Afirka ya bayyana a matsayin wani yunkuri na tauye ‘yancin yada labarai a kasar.

Daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin wato Samira Sabou, ita ce shugabar kungiyar ‘Association of Bloggers for Active Citizenship ABCA’ wato ‘kungiyar masu wallafa labarai da sauran abubuwan wayar da kan jama’a ‘yan kishin kasa a kafofin intanet’, yayin da Moussa Aksar ke matsayin mamallakin jaridar L’Evenement kuma shugaban Cibiyar Norbert Zongo da ta kunshi ‘yan jarida masu bincike a yammacin Afirka wato CENOZO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.