Isa ga babban shafi
Sudan - zanga-zanga

Jami'an tsaro sun tsare shugaban tashar Aljazeera a Sudan

Jami’an tsaron Sudan sun kama shugaban ofishin gidan talabijin na Aljazeera mallakin kasar Qatar a wannan  Lahadin, kwana guda bayan wani sabon farmakin da aka kai kan masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida.

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin soji a Sudan 7/11/21.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin soji a Sudan 7/11/21. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Wannan dai na daya daga cikin kwanaki mafi zubar da jini tun bayan juyin mulkin na baya-bayan nan a Sudan kusan makonni uku da suka gabata.

"Jami'an tsaro sun kai samame gidan Al-Musalami al-Kabbashi, shugaban ofishin Al Jazeera a Sudan, inda suka tsare shi," in ji kafar sadarwar ta Twitter ba tare da wani karin bayani ba.

Matakin sojojin ya janyo tofin Allah tsine daga kasashen duniya da kuma zanga-zangar da 'yan Sudan suka yi a kai a kai, inda suke neman maida Mulki ga fareren hula.

Al Jazeera na bibiyar zanga-zangar adawa da juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba, amma a makon da ya gabata ta kuma gabatar da cikakkiyar hira da shugaban sojin Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ke zama daya daga cikin hirar sa da manema labarai ta biyu kacal da yayi.

Hari kan Kafafen watsa labarai 

Bayaga tashar Al Jazeera, ana kai wa wasu kafafen yada labarai hari tun bayan juyin mulkin, lokacin da Burhan ya ayyana dokar ta-baci, ya tsare shugabannin farar hula tare da tsige gwamnatin da aka kafa bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir na watan Afrilun shekarar 2019

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.