Isa ga babban shafi
Nijar-Zabe

Sadarwar intanet ta daidaita a Nijar bayan shafe kwanaki 10 a katse

Sadarwar intanet ta sake daidaita a jamhuriyar Nijar bayan katseta da hukumomin kasar suka yi tsawon kwanaki 10, sakamakon rikici da ya biyo bayan sakamakon zaben shugabancin kasar da ya bayyana dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hoto domin misali dake nuna turken dake inganta sadarwar layukan Intanet.
Hoto domin misali dake nuna turken dake inganta sadarwar layukan Intanet. © TT News Agency/Adam Ihse/via REUTERS
Talla

Akalla mutane 2 suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da ta biyo bayan nasarar ta Bzoum Muhammad da ya lashe kashi 55.7 na kuri’un da aka kada, yayin da Mahaman Ousman na RDR Canji ya samu kashi 44.

Bayanai sun ce an soma samun daidaitar sadarwar ta Intanet a jamhuriyar ta Nijar ne da misalin karfe 11 na  daren ranar Juma’a.

Sai dai har zuwa wannan lokaci babu karin bayani daga kamfanonin sadarwa da kuma hukumomin na Nijar, dangane da daukar matakin da ya sanya wasu kungiyoyin fararen hula shigar da kara kotu.

Wata kididdiga ta nuna cewar katse sadarwar ta Intanet a Nijar ya janyowa kamfanonin sadarwa a kasar hasarar kimanin CFA miliyan 80 duk rana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.