Isa ga babban shafi
Zaben - Nijar

Bazoum ya lashe zaben shugaban kasar Nijar

Tsohon Ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya lashe zaben shugaban kasar da akayi zagaye na biyu sakamakon nasarar da ya samu da kuri’u kashi 55.75 sabanin na abokin karawar sa kuma tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane wanda ya samu kashi 44.25

Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed
Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed Niger Search
Talla

Shugaban hukumar zabe Issaka Souna ya gabatar da sakamakon, yayin da ya bayyana cewar sakamakon zai tabbata ne lokacin da kotun fasalta kundin tsarin mulki ta tabbatar da shi.

Kafin gabatar da sakamakon, manajan yakin neman zaben Ousmane, Falke Bacharou yayi zargin tafka magudi, inda ya bukaci magoya bayan su da su fito zanga zanga kan tituna.

Kungiyoyin da suka sanya ido kan zaben cikin su harda kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS sun bayyana gamsuwa da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, idan banda hadarin da aka samu lokacin da motar jami’an hukumar zabe ta taka nakiya a Tillaberi, abinda ya kaiga mutuwar mutane 7.

Wannan zabe ba karamar nasara ba ce ga Jamhuriyar Nijar daya daga cikin kasashen Afirka ad suka yi suna wajen tafiyar da dimokiradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.