Gidan wakilin RFI sashen Faransanci ya gamu da fishin masu zanga-zanga a Nijar
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce masu zanga zanga suka kona gidaje da shagunan jama’a da dama ciki har da gidan wakilin sashin faransanci na Radio France International Rfi a birnin Yamai, Musa Kaka.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya shaida yadda masu zanga-zangar fiye da 200 suka yiwa gidan wakilin na RFI Musa Kaka dirar mikiya a jiya Alhamis tare da kwasar ganima baya ga kone daukacin gidan.
Wannan dai na matsayin jerin tashe-tashe hankulan Zabe da Nijar ba ta saba gani ba a tarihi, dai dai lokacin da a karon farko farar hula karkashin mulkin Demokradiyya ke Shirin mika Mulki ga zababben shugabar farar hula a kasar
Musa Kaka da ke matsayin wakilin Rfi na tsowon lokaci a Jamhuriyar ta Nijer, ya taba share kusan shekara garkame a gidan yari daga 20 ga watan Satumban 2007 zuwa 23 ga watan Yulin 2008 sakamakon zargin da gwamnatin marigayi Tanja Mammadu ta yi masa cewa, yana da alaka da ‘yan tawayen abzinawan yankin arewacin kasar.
Tuni dai hukumar gudanarwar RFI ta mayar da martani cewa, an kai wa wakilin na ta hari ne a matsayinsa na dan jarida, wanda hakan ke zama mummunan taka ‘yancin aikin jarida.
Hukumar gudanarwar RFI da ke bayyana goyon baya ga ma’aikacin na ta, ta kuma yi tir da aika-aikar yayinda ta sha alwashin ci gaba da kare ‘yancin aikin samar da labarai a Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu