Isa ga babban shafi
Nijar

Harin bam ya kashe jami'an hukumar zaben Nijar bakwai

Harin bam ya kashe jami'an hukumar zaben Nijar bakwai, bayan taka nakiya da motarsu tayi a yankin Tillaberi gaf da iyakar kasar da Mali.

Motar jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi
Motar jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi RFI Hausa/ Salisu Issa
Talla

Yayin karin bayani kan aukuwar lamarin, gwamnan yankin na Tillaberi Tijjani Ibrahim Kachalla yace wasu jami’an hukumar zaben ta CENI guda uku sun jikkata sakamakon taka nakiyar.

Taka nakiyar da jami’an suka yi, ya zo ne a daidai lokacin da zaben shugaban kasa zagaye na biyu ke gudana a Jamhuriyar Nijar.

Jami’an na kan hanyarsu da zuwa yankin Tillaberi dan sa ido kan zaben dake gudana ne a lokacin da motarsu ta taka nakiyar.

Tun shekarar 2017 yankin Tillerberi ke karkashin dokar ta baci, sakamakon fuskantar hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

Hari na karshe mafi muni da ‘yan bindiga suka kai a yankin na Tillaberi dai shi ne wanda suka kashe kimanin mutane 100, bayana kaiwa wasu kauyuka biyu farmaki.

Yayin zaben shugabancin Jamhuriyar Nijar da ya gudana a wannan Lahadi an fafata ne tsakanin ‘yan takara guda biyu, tsohon shugaban kasa Mahaman Ousmane na jam’iyyar RDR Canji, da kuma Bazoum Muhammed na jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.